Home Labarai An kori ƴan sanda 10 kan saɓa ƙa’idar aiki

An kori ƴan sanda 10 kan saɓa ƙa’idar aiki

146
0

Rundunar ƴan sanda ta jihar Lagos, ta kori jami’anta 10 sakamakon aikata laifuka daban-daban.

Mai magana da yawun rundunar SP Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

A cewarsa, an kori jami’an ne a ƙoƙarin da ake na tabbatar da ɗa’a da kuma kare martabar aikin ɗan sanda a jihar.

Adejobi ya ce rundunar ta gurfanar da jami’ai 81 a gaban kwamitin ladabtarwa a tsakanin watan Oktoban 2019 zuwa na 2020, kan aikata laifuka daban-daban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply