Jami’ai a birnin Columbus na jihar Ohio, Amirka, sun ce a kori wani ɗan sanda da ya harbe wani mutum baƙar fata har lahira a makon jiya.
Mutuwar mutumin mai suna Andre Maurice Hill, ta ƙara ririta wutar zanga-zangar da ake kan muzgunawar ƴansanda da kuma salon nuna ƙyama da ake wa baƙar fata a ƙasar.
Shugaban ƴansandan Birnin Columbus Thomas Quinlan, ya ce an kori Jami’i Adam Coy, wanda da farko dakatar da shi aka yi, bayan hujjojin da aka samu waɗanda sun isa a kore shi.
