Home Labarai An kori dalibar POLAC Wudil bayan an same ta da juna-biyu

An kori dalibar POLAC Wudil bayan an same ta da juna-biyu

169
0

Babban kwamandan kwalejin horas da ‘yansanda ta Wudil jihar Kano AIG Zanna M. Ibrahim ya ce sun kori wata daliba bayan da aka same ta ta yi ciki wanda ya saba da dokar zama dalibi a kwalejin.

AIG Zanna M. Ibrahim da ya ke magana a wajen bikin marhabin da sabbin daliban kwalejin, ya ce an kuma kori karin wasu dalibai 24, bisa samunsu da laifin rashin da’a.

Ya ce kwalejin za ta bullo da tsarin yi wa dalibai gwajin kwayoyi da na juna biyu a duk lokacin da suka koma hutu kafin su ci gaba da karatu don tabbatar da sahihancin lafiyarsu.

AIG Zanna ya kuma bukaci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu daliban kwalejin su 4 ‘yan ajin karshe bisa zargin tu’ammali da miyagun kwayoyi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply