Home Labarai An kori jami’in tsaron ofishin jakadancin Nijeriya a Jamus

An kori jami’in tsaron ofishin jakadancin Nijeriya a Jamus

118
0

An kori wani mai kula da lamurran tsaro a Ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Jamus, Martins Oni.

A watan Nuwamba ne, aka dakatar da Oni bayan da aka kama shi a cikin wani bidiyo yana neman yin lalata da wata kafin ya bata fasgo.

A cikin bidiyon wanda ya janyo cecekuce bayan ya shiga kafafen intanet, anga jami’in a dakin otal inda ya shirya haduwa da matar don yin lalata da ita kafin ya taimaka mata wajen samun fasgon.

Tun a lokacin Jakadan Nijeriya a Jamus, Yusuf Tuggar, ya bada umurinin gudanar da binciken jami’in tsaron tare da alkawarin hukunta shi matukar aka kama shi da laifi.

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar a ranar Talata, ya ce an kama Oni da laifin da ake zarginsa da kuma karya ka’idojin aikinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply