Home Labarai An kori ‘yarsanda daga aiki saboda ta yi ciki kafin aure

An kori ‘yarsanda daga aiki saboda ta yi ciki kafin aure

42
0

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kori wata ‘yarsanda mai igiya biyu “corporal” Omolola Olajide daga aiki bayan da ta samu juna-biyu tana budurwa bata yi aure ba.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani sakon ‘yansanda mai lamba CJ:4161/EKS/IY/Vol.2/236, DTO:181330/01/2021 da jaridar Punch ta samu kwafi.

Sakon dai ya fito ne daga sashen kula da kudi na rundunar ‘yansandan Ekiti, aka aike wa babban baturen ‘yansanda na Iye Ekiti inda Omolola ke aiki.

Takardar ta nuna cewa Omolola ta kammala samun horon aikin dansanda a shekarar 2020, sannan aka tura ta aiki a caji ofis na Iye Ekiti.

Rundunar ‘yansandan ta bukaci jami’in kula da kudinta, da ya aike da bayanan Omolola ga maau kula da tsarin biyan albashi na IPPIS domin dakatar da albashinta.

Takardar tace abin da Omolola ta yi ya saba kundin aikin dansanda mai lamba ta 127 na hana mata su samu juna biyu kafin su yi aure.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply