Home Labarai An kubutar da wani mutum da ya shekara 15 daure a Sokoto

An kubutar da wani mutum da ya shekara 15 daure a Sokoto

110
0

Mai ba gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shawara kan harkokin jin kai da kiyaye hakkin dan’Adam Hajiya Ubaida Muhammad Bello ta ce sun samu labarin wani mutum mai suna Salisu Muhammad mai shekara 45 cewa an daure shi na tsawon shekara 15 a garin Gidan Madi cikin karamar hukumar Tangaza da ke jihar.

Hajiya Ubaida ta ce, makwabtan mutumin ne suka kwarmata bayanan da suka sa aka gano shi da ake tunanin ma ko ya rasu.

“Mun same shi cikin mawuyacin hali fitsari da komai nan yake yi ba wata kulawa da ya ke samu.” A cewarta.

‘Yansanda a jihar ne suka kubutar da shi, mai magana da yawun rundunar ta jihar Sakkwato ASP Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin kuma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply