Home Labarai An kwace kaya na sama da milyan 270,000 a jihar Jigawa

An kwace kaya na sama da milyan 270,000 a jihar Jigawa

85
0

Abdullahi Garba Jani

Karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa hadin guiwa da hukumar kula da tsaftace muhalli ta jihar sun kwace tare da kone kayan da suka lalace na kudi sama da Naira milyan 270,000.

Da ya ke magana a wajen lalata kayan a Hadejia, shugaban karamar hukumar Alh Muhammad Mai Kanti ya shawarci ‘yan kasuwa da su tabbatar da sun sayo kayan da ba su lalace ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya-NAN- ya ruwaito Alh Muhammad na bukatar masu sayen kaya da a kodayaushe su rika kai rahoton ‘yan kasuwar da suke sayar da kayan da suka lalace( expired product) don daukar mataki.

Ya ja kunnen ‘yan kasuwa da su daina baza kayansu a sarari da barin kayan a cikin rana da hakan ke rage wa kayan nagarta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply