Home Labarai An maka Atiku kotu kan bashin milyan 500 kudin kamfen

An maka Atiku kotu kan bashin milyan 500 kudin kamfen

310
0

Wasu kamfanoni guda biyu sun maka tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben kasa na 2019 Atiku Abubakar wata babbar kotu a garin Abuja kan bashin kudin kamfen har Naira milyan 500.

A sammacen da sakataren kotun Danmusa Williams ya saka wa hannu, an bukaci tsohon shugaban kasar da daraktan kamfen nasa Nat Yaduma da su gurfana gaban kuliya saboda kin biyan kudaden bayan shekara 2 da wucewar wa’adin yarjejeniyar.

Bayan tuntubar mai ba Atiku shawara kan harkar watsa labarai Paul Ibe ya bayyana cewa jam’iyyar ta PDP da ya tsaya takara a cikinta ce ya kamata a tuntuba kan wannan batu.

Shi kuwa sakataren jam’iyyar ta PDP na kasa Kola Ologbondiyan ya shaida cewa Ibe ne ke da alhakin ba da ba’asin abin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply