Home Labarai An maka CBN kotu kan rubutun ajami a kuɗin Nijeriya 

An maka CBN kotu kan rubutun ajami a kuɗin Nijeriya 

233
0

Wani lauya da aka bayyana sunansa da Malcolm Omirhobo ya maka babban bankin Nijeriya CBN a wata kotu da ke jihar Legas inda yake so a tilastawa bankin da hanzarta cire harufan larabci na ajami da ake kan kudaden kasar.

Malcolm ya bukaci a maye gurbin harufan na Larabci da daya daga cikin manyan harsunan kasar; Hausa, Yoruba ko kuma Igbo.

Rubutun ajami da ke jikin kudade ya dade yana samun suka, inda da dama ke alakanta shi da addinin musulunci.

To sai dai tuni gwamnan babban bankin Nijeriya Mista Godwin emefiele ya musanta cewa harufan na Larabci basa nuni da cewa alama ce ta Musulunci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply