An nada Mai shari’a Abbas Bawale na kotun shari’a ta uku a matsayin wanda zai cigaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Katsina ta shigar da tsohon gwamna Ibrahim Shema bisa zargin facaka da kudin jihar.
Gwamnatin jihar ta Katsina dai, na zargin tsohon gwamna Shema da karin wasu mutane 4 da wadaka da kudaden gwamnati da suka kai darajar bilyan 11 mallakar kananan hukumomi.
Tun da farko dai, Mai shari’a Maikaita Bako ne ke jagorantar karar, amma a farkon shekarar nan, Allah Ya karbi ransa a farkon wannan shekarar.
