Mai Martaba Sarkin Daura Alh Umar Farouk Umar ya nada Alhaji Salisu Abdullahi sarautar Baushin Daura, sai kuma Abdullahi Lawal a matsayin Wazirin Baushi.
Sarkin labarai na masarautar Daura Alhaji Usman Ibrahim Yaro ne ya shaida wa DCL Hausa da yammacin Asabar din nan.
A farkon watan Nuwambar nan ne dai Allah ya yi wa tsohon Baushi a masarautar Alhaji Lawal Abdullahi rasuwa.
