Gwamnan jihar Nasarawa Engr Abdullahi Sule ya amince da nadin Barrister Muhammad Ubandoma a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan Mal Ali Abare ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Idan za a iya tunawa dai, a cikin wannan makon ne gwamnan ya fitar da sanarwar sauke tsohon sakataren gwamnatin jihar.
