Home Lafiya An nada sabon Sallaman Katsina

An nada sabon Sallaman Katsina

211
0

Majalisar Masarautar Katsina ta amince da nadin Alhaji Kabir Ummaru ‘Yar’adua a matsayin sabon Sallaman Katsina.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman a Katsina.

Takardar ta ce za a sanar da ranar da za a nada sabon Sallaman na Katsina nan gaba.

Nadin sabon Sallaman na Katsina ya biyo bayan nada Alhaji Bello Mamman Ifo da aka yi a matsayin Sarkin Yakin Katsina, hakan ta faru kuwa saboda rasuwar Sarkin Yakin Alhaji Bashir Mamman Ifo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply