Home Labarai An nada sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Katsina

An nada sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Katsina

192
0

Gwamnatin jihar Katsina ta nada Alhaji Mustapha Muhammad Surajo a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatare mai kula da sashen mulki a ofishin shugaban ma’aikatan jihar, Usman Isyaku Dutsinma.

Sanarwar ta ce an nada Mustapha Muhammad wannan mukami ne, bayan cin jarabawar da kwamitin zartaswar hukumar ya yi masa.

Mustapha Muhammad Surajo dai ma’aikaci ne a hukumar tattara haraji ta kasa FIRS.

Takardar ta ce nadin nasa zai fara aiki ne a 1 ga Janairun 2021, wanda zai gaji Aminu Danrabati Abdulmumin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply