Home Kasashen Ketare An nemi a daure ‘yar jarida da tarar miliyan daya na CFA...

An nemi a daure ‘yar jarida da tarar miliyan daya na CFA a Yamai

193
0
Samira Sabou 'yar jarida a Nijar
Samira Sabou 'yar jarida a Nijar

A safiyar Talatar nan ne masu shigar da kara a wata babbar kotu da ke babban birnin Yamai suka nemi a daure fitacciyar ‘yar jaridar Nijar Samira Sabou da ta yi suna a shafukan sada zumunta na zamani a gidan yari har na wata guda da sati daya da kuma biyan tarar miliyan daya na CFA

Tun a ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata ne dai ake tsare da ‘yar jaridar sakamakon gurfanar da ita da aka yi biyo bayan wani labari da ta wallafa wanda d’an shugaban kasar Nijar Sani Mahamadou Issoufou ya yi zargin ta bata masa suna.

Samira Sabou 'yar jarida a Nijar
Samira Sabou ‘yar jarida a Nijar

A ranar 28 ga wannan wata da muke ciki mai zuwa ne dai alkali zai fitar da sakamakon karshen shari’ar inda Samira Sabou za ta san makomarta.
A kwanakin baya dai kungiyar Amnesty International ta yi kira da a saki ‘yar jaridar, tana mai cewa babu komai a cikin kamun ‘yar jaridar illa tsagwaran siyasa da tauye hakkin aikin jarida.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply