Home Addini An raba Zakkar Naira miliyan 100 a Hadejia

An raba Zakkar Naira miliyan 100 a Hadejia

154
0

Kwamitin da ke tattara Zakka na masarautar Hadejia ta jihar Jigawan Nijeriya ya sanar da cewa a shekarar musuluncin da ta shude ya karbi zakkar amfanin gona da dabbobi hadi da kudaden da suka kai kimanin Naira milyan dari daga attajirai da ma yan kasuwa. Kawo yanzu kuma an rarraba wa talakawan yankin wadannan kadarori a matsayin Zakka.

Shugaban kwamitin Barista Abdul-fatah Abdul-wahab ne ya sanar da haka lokacin da ya kaddamar da bikin fara raba zakkar ta wannan sabuwar shekarar musulunci a garin Hadejia. Ya ce ya zuwa yanzu kwamitin ya raba Zakkar ga mabukata fiye da 29,000.

Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje ya yaba wa attajiran yankin da suka fitar da Zakkar domin sauke nauyin da ke kansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply