Home Sabon Labari An rufe daukacin makarantun kwana na Katsina

An rufe daukacin makarantun kwana na Katsina

1893
2

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umurnin a rufe daukacin makarantun kwana da ke jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan sace dalibai ‘yan makarantar kwana ta kimiyya da ke Kankara da ‘yan bindiga suka yi a daren Juma’a.

Gwamnan ya ba da wannan umurnin ne a safiyar Asabar a lokacin da ya ziyarci makarantar bayan ya gana da iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki na makarantar.

Gwamnan ya ba mutanen yankin hakuri da ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa don ceto sauran yaran.

SAUTI:http://https://www.facebook.com/watch/?v=718785938770481

 

Labarai Masu Alaka: Labari na musamman: yadda ƴanbindiga suka sace ɗalibai a Ƙanƙara, Katsina

Buhari ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindiga a makarantar Katsina

Rashin tsaro – Ƴanbindiga sun kori mutane daga gidajensu a Katsina

An rufe daukacin makarantun kwana na Katsina

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

2 COMMENTS

  1. Maganar gaskiya gwamnatin Nigeria tasa hukuncin kisa ga duk wasu laifuffuka kamar haka.Fyade. Informer. Kidnapped. Kaura . Satar kudin gwamnati. Ko wanene ko Dan wanene.na gode

  2. Gwamnati jiha Mai adalci akarkashin adalin Gwamna Mai tsoran Allah. Yana shifka wasu na tonewa. Allah don karfin mulkinka don kudirarka don soyayyarka da manzonka Annabi Muhammadu saw duk Mai sa hannu akan wannan tarzoma Allah ka wulakantashi ka Tozartashi

Leave a Reply