Home Labarai An rufe makarantun kwana a jihar Neja

An rufe makarantun kwana a jihar Neja

33
0

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya bada umurnin gaggauta rufe makarantun kwana da ke yankunan da ake fama da matsalolin ‘yanbindiga a jihar.

Gwamnan ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi domin kare rayukan daliban da ke yankunan da ‘yanbindigar suka mamaye.

Gwamnan wanda ya bayyana haka bayan wani takaitaccen taro da suka da hukumomin tsaro a gidan gwamnatin jihar da ke Minna, ranar Larabar nan, ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki duk matakin da ya dace don shawo kan matsalar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply