Home Labarai An sace manoma 50 a Zamfara

An sace manoma 50 a Zamfara

147
0

A wannan Lahadi, al’ummar garin Lingyadi da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara arewa maso yammacin Nijeriya, sun ce wasu mahara sun sace sama da mutane 50 a yankin lokacin suna aikin gona misalin karfe takwas na safiya.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da sace mutanen, sai dai ta ce har yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba kamar yadda kwamishinan tsaro da lamuran cikin gidan jihar Abubakar Justice Dauran ya shaida wa DCL Hausa

Kwamishinan ya ce tuni suka tura Jami’an tsaro domin gano adadin mutanen da kuma karbo su daga maharan. Ya kuma jaddada kokarin gwamnatin jihar na ci gaba da samar da tsaro kamar yadda take ta fafutukar yi tun lokacin da suka kama madafun iko.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply