Home Labarai An sace shugaban kungiyar kwadago na Taraba

An sace shugaban kungiyar kwadago na Taraba

28
0

Wasu da ba a san ko su wanene ba, sun sace shugaban kungiyar kwadago na jihar Taraba Peter Jediel.

DCL Hausa ta gano cewa an sace shugaban kungiyar ne da sanyin safiyar Lahadin nan a gidansa da ke yankin Sunkani karamar hukumar Ardo-Kola.

Kanin shugaban kungiyar Mr Fidelis Jediel ya shaida wa ‘yanjarida cewa ‘yan bindigar sun mamaye hanyar zuwa gidan, suka yi awon-gaba da shi.

Har ya zuwa lokacin hada labarin, babu wata tartibiyar magana daga hukumar ‘yansandan jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply