Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce za a dawo da sufurin jiragen saman ƙasashen waje a ranar 29 ga watan Agusta.
Ministan sufurin sama Sanata Hadi Sirika ya bayyana haka ranar Litinin, a shafinsa na Twitter.
Sanatan ya ce tsarin sufurin saman zuwa ƙasashe zai zama kamar wanda ake amfani da shi a sufurin cikin gida.
Ya ce za a fara tashin jirage zuwa ƙasashen duniya da shigowarsu Nijeriya a filayen jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma na Murtala Muhammad da ke Lagos.
