Home Labarai An saka ranar gudanar da zaben kananan hukumomi a Yobe

An saka ranar gudanar da zaben kananan hukumomi a Yobe

38
0
Mai Mala Buni Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da ranar 27 ga watan gobe Fabarairu a matsayin ranar gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar.

Shugaban hukumar zaben jihar Dr Mamman Mohamed ya sanar da hakan ga manema labarai a Damaturu babban birnin jihar.

Yace ana kyautata zaton mutane 1,365,000 ne za su kada kuri’a a zaben da za a zabi shugabannin kananan hukumomi 17 da kansiloli 178.

Mamman Mohamed ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su bada hadin kai don gudanar da zaben cikin nasara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply