Home Coronavirus An saka ranar komawa makarantu a Katsina, karatun boko 8:00am zuwa 3:00pm

An saka ranar komawa makarantu a Katsina, karatun boko 8:00am zuwa 3:00pm

1264
0

Ma’aikatar ilmi ta jihar Katsina, ta ce daliban ajin karshe na makarantun firamare da karamar sakandare da masu rubuta WAEC za su koma makaranta a ranar Litinin 10 ga wannan wata.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Salisu Lawal Qerau, ta ce daliban makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 9 ga wata.

Ma’aikatar ta wajabta cewa dukkanin malamai da dalibai sai sun saka takunkumin rufe hanci da guje wa cudanya da sauran matakan kariya daga corona.

Kazalika, takardar ta ce an kara tsawaita lokacin makaranta daga 8:00 na safe zuwa 3:00 na yamma, kuma daga Litinin zuwa Asabar

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply