Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi An sake sabunta wa’adin shugaban ITF

An sake sabunta wa’adin shugaban ITF

134
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake amincewa da nadin babban daraktan asusun kula da sanin makamar aiki, (ITF) Sir Joseph Ntung Ari zuwa wa’adin shekaru hudu.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren din-din din na Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Nasir Sani-Gwarzo.

Idan za a iya tunawa an nada Mista Ari a matsayin Darakta ne a shekarar 2016 wanda kafin a sabunta masa mukamin wa’adinsa na dab da karewa.

Nadin nasa zai fara aiki ne daga 26 ga Satumba, na wannan shekara ta 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply