Home Labarai An saki ‘yan fursuna 300 a Katsina

An saki ‘yan fursuna 300 a Katsina

144
0

Katsina: AN SAKI YAN GIDAN YARI 300.

Babban Alkalin Alkalan jihar Katsina justice Musa Danladi ya shaidawa jaridar The Nation cewa kawo farkon makon nan ya bayar da umarnin sakin fursunoni 300 da ke zaman wakafi a gidajen yarin Katsina.

Babban jojin ya ce wannan na daga cikin sauye-sauye na ci gaba da yake da burin aiwatarwa a harkar sharia a jihar Katsina.

Jamaan da aka saki din dai jamaa ne da su suka aikata wasu laifuka da basu taka-kara-sun karya ba, amma kuma saboda wasu dalilai aka garkamesu a gidan yari.

Shin kuna zaunawa kuyi tunanin yadda rayuwar yan fursuna ke gudana, babu yawo,babu buga waya, babu chatting, babu sauran yanci?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply