Home Labarai An sako shugaban ma’aikatan Edo bayan an biya kudin fansa

An sako shugaban ma’aikatan Edo bayan an biya kudin fansa

100
0

Masu garkuwa da mutane da suka yi awon-gaba da shugaban ma’aikatan Jihar Edo Mista Anthony Okungbowa, sun sako shi.

A ranar 20 ga Disambar nan DCL Hausa ta ba da labarin cewa; wasu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da Okungbowa a ranar Asabar a kan titin Oza na karamar hukumar Orhionmwon da ke jihar, ya yin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa daga Benin bayan halartar wani taro da wani dan siyasa ya shirya.

Wata majiyar daga danginsa ta bayyana cewa wadanda suka sace Okungbowa din sun sake shi ranar Litinin.

Majiyar ta ce an saki Okungbowa ne bayan an biya kudin fansa da masu garkuwar suka nema.

Sai sai majiyar ba ta ambaci adadin kudaden da aka biya ba a matsayin fansa.

Kazalika an ce an biya kudin fansar ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin dangin Okungbowa da kuma gwamnatin jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply