Home Labarai An sako ‘yan kasuwar Kano bayan biyan kudin fansa

An sako ‘yan kasuwar Kano bayan biyan kudin fansa

48
0

Mahukuntan kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari jihar Kano sun tabbatar da sakin ‘yan kasuwar 27 da aka yi garkuwa da su kan hanyar su ta zuwa garin Aba na jihar Abia.

Mai magana da yawun kungiyar ta Kantin Kwari Mansur Haruna Dandago ya tabbatar da cewa an sako ‘yan kasuwar ne bayan an biya kudin fansa.Sai dai bai bayyana ko nawa ne aka biya ba kafin a sako su.

Yace ‘yan kasuwar na kan hanyarsu ta komawa Kano, kuma dukkanjnsu ne aka sako, sannan su na cikin koshin lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply