Home Lafiya An sallami masu jinyar Covid-19 3 a Kaduna

An sallami masu jinyar Covid-19 3 a Kaduna

86
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna ta bada sanarwar sallamar mutum 3 da aka tabbatar sun warke daga cutar Covid-19.

Wata sanarwa da Kwamishinar lafiya ta jihar Dr Amina Mohammed-Baloni ta fitar da yammacin jiya, ta ce an sallame su ne bayan an gano sun warke sarai daga cutar.

Mutanen dai na cikin mutum shida da aka tabbatar sun kamu da cutar, wanda yanzu haka aka sallami mutum huɗu da suka warke.

Kwamishinar ta ce yanzu mutum biyu ne suka rage waɗanda ke ɗauke da cutar a jihar, kuma ana sa ran sallamar su nan ba da jimawa ba.

Haka kuma, Baloni ta yabawa ƙoƙarin jami’an kiwon lafiya, jami’an bin diddiƙi, wakilan kwamitin gaggawa da dai sauran masu ruwa da tsaki, da suka bada gudunmuwa kan wannan nasara da aka samu.

Ta kuma shawarci jama’ar jihar da zu ci gaba da ɗaukar matakan kariya daga kamuwa da cutar, tana mai cewa riga-kafi ya fi magani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply