Home Coronavirus An samar da jami’ai 3,300 don gudanar da binciken Covid-19 a Kano

An samar da jami’ai 3,300 don gudanar da binciken Covid-19 a Kano

230
0

Shugaban tsare tsare na kwamitin shugaban ƙasa kan Covid-19 Dr Sani Aliyu ya ce an samar da jami’an kwarmato 3,300 domin gudanar da binciken gida-gida don gano masu ɗauke da cutar a Kano.

Da yake magana a wajen bayanan kwamitin na kullum, Sani ya ce kwamitin ya ƙara samun tawaga 20 ta masu kai ɗauki ga ɓarkewar cutar ta hannun abokan hudɗar su don tabbatar da gwajin mutane a Kano.

Da yake magana shima, shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce dole ne yanzu hankali ya koma Kano, saboda ƙaruwar mutanen da ake samu na ɗauke da cutar a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply