DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeBabban Labari An samu bullar cutar mashako 'diphteria' ga kananan yara a asibitin koyarwa...

An samu bullar cutar mashako ‘diphteria’ ga kananan yara a asibitin koyarwa na Katsina

Asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke jihar Katsina na fama da karuwar kananan yara masu dauke da cutar mashako ta ‘diphteria’, inda adadin marasa lafiya a cibiyar killace masu cutar ya kai kimanin 70, alhali cibiyar na da gadaje 15 kacal, lamarin da ya tilasta kwantar da wasu yara a kasa domin ba su kulawa.

Jami’in hulda da jama’a na asibitin, Abidu Yunusa, ya tabbatar wa DCL Hausa da barkewar cutar, yana mai cewa iyaye na tururuwa zuwa asibitin da ‘ya’yansu da ke fama da cutar domin samun kulawar likitoci.

Yunusa ya ce cibiyar killace masu cutar tana da gadaje 15 ne kacal, yayin da adadin marasa lafiyar da ke bukatar kulawa ya kai kimanin 70. Ya ce karancin gadaje da yawan marasa lafiya ya kai ga ana kwantar da wasu yara a kasa domin ba su magani.

Ya kuma tabbatar da cewa an samu asarar rayuka sakamakon barkewar cutar, sai dai ya ce ba zai iya bayar da takamaiman adadin wadanda suka mutu nan take ba.

A wani bangaren, wata majiya daga cikin asibitin da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa DCL Hausa cewa an kwantar da yara 31 masu fama da cutar a cikin mako guda, abin da ke nuna yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar cikin sauri.

Majiyar ta ce ya zuwa ranar Juma’a, yara 14 na kwance a asibitin, yayin da wasu tara ke jiran a kwantar da su. Ta ce an fara ganin karuwar masu kamuwa da cutar tun a watan Yulin 2026, duk da cewa ana samun bullar cutar lokaci zuwa lokaci a shekarun baya.

Cutar diphtheria, wadda aka fi sani da mashako a Hausa, cuta ce mai saurin yaduwa da kwayoyin bacteria ke haddasawa. Cutar kan haifar da zazzabi da kumburin makogwaro da hangum, wanda kan sa hadiye abinci ko ruwa da numfashi su yi wahala. A lokuta masu tsanani, cutar na iya haddasa mutuwa.

A cewar kwararru a fannin lafiya, kwayoyin cutar mashako na iya samar da wata guba mai hatsari da kan yi illa ga zuciya, koda da jijiyoyin jiki. Ana iya amfani da magungunan antibiotics wajen kashe kwayoyin cutar, tare da maganin antitoxin domin dakile gubar da take samarwa. Haka kuma, ana killace masu dauke da cutar domin rage yaduwarta.

Majiyar asibitin ta nuna damuwa kan rashin samun rigakafi tsakanin yaran da ke kamuwa da cutar, inda ta kiyasta cewa kusan kashi 99 cikin 100 na sabbin yaran da ake samu da cutar a asibitin ba su samu rigakafi ba, kuma da yawa daga cikinsu sun fito ne daga iyalai marasa karfi.

Wani kwararre a fannin lafiya, Farfesa Usman Yusuf, ya ce ana iya kare yara daga cutar mashako ta hanyar yi musu rigakafi tun suna kanana. Sai dai ya ce karancin yaran da ake yi wa rigakafi na barin yara da dama cikin hadarin kamuwa da cutar, tare da bai wa cutar damar yaduwa cikin al’umma.

Farfesa Yusuf ya danganta karancin samun rigakafin da matsaloli da dama da suka hada da rashin tsaro, talauci, kaura daga kauyuka zuwa birane, karancin wayar da kan iyaye da kuma rashin bai wa harkokin kiwon lafiya na matakin farko muhimmancin da ya dace a mataki na kasa.⁸

Ya yi gargadin cewa muddin yawan yaran da ake yi wa rigakafi ya ci gaba da raguwa, al’umma ba za ta samu isasshen kariya daga yaduwar cututtuka ba, lamarin da zai ci gaba da jefa yara cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake iya kare su daga gare su ta hanyar rigakafi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata