Home Labarai An samu karin kananan hukumomi masu fama da ta’addanci a Sakkwato

An samu karin kananan hukumomi masu fama da ta’addanci a Sakkwato

95
0

Yayin da ake kara samun kamarin hare-haren ‘yan bindiga a wasu kananan hukumomin jihar Sakkwato, yanzu haka karamar hukumar Tangaza da Gudu sun shiga jerin kananan hukumomin da ke fama da wannan matsala.

‘Yan bindiga dai suna kan kassara yankin inda yanzu suke ci gaba da Kai hare-hare ga mazauna yankunan karkara da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Hon Yusuf Isah Kurdula, shi ne dan majalisar wakilai da ke wakiltar kananan hukumomin Tangaza da Gudu kuma ya roki gwamnatin tarayya da ta kawo masu dauki kan ‘yan bindiga su iyar da kare su.

Ko da ya ke, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Sakkwato Muhammad Sadiq Abubakar ya tabbatar da cewa ko a ranar Larabar da ta, gabata sun gudanar da taro da masu ruwa da tsaki a yankunan da ke fama da matsalar tsaro don shawo kan ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply