Home Coronavirus An samu matasan NYSC 2 dauke da corona a Kano

An samu matasan NYSC 2 dauke da corona a Kano

114
0

Jami’ar kula da shirin matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Kano Aisha Tata, ta ce an samu matasan NYSC 2 dauke da cutar corona a Kano.

A wajen bikin marhabin da matasan na NYSC ‘yan rukunin “B” kaso na daya “stream 1), Aisha Tata ta ce an tura sabbin matasan NYSC 826 a sansaninsu da ke Karaye, Kano.

Ta ce an gaggauta gwada matasan bayan da suka shiga sansanin, har ma an mika su ga hukumomin da suka dace domin kula da lafiyarsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply