Gwamnan jihar Jigawa Alh. Muhd Badaru Abubakar yace an samu mutum na farko a jihar da ya kamu da cutar COVID-19 daga karamar hukumar Kazaure.
Gwamnan ya bayyana haka ne yau Lahadi a fadar gwamnatin jigawa, ya yin da ya ke ganawa da manema labarai.
Gwamna Badaru yace a sabo da haka karamar hukumar kazaure za ta zamo kulle tun daga wannan rana ta lahadi zuwa tsawon mako guda.
