Home Labarai An samu rahoton tashin gobara 173 a Kebbi

An samu rahoton tashin gobara 173 a Kebbi

19
0

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kebbi, ta ce ta samu rahoton tashin gobara 173 tare da mutuwar mutum guda, a shekarar 2020.

Daraktan Hukumar Alhaji Yahaya Zazzagawa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a ranar Talata cewa gobarar ta faru ne tsakanin watan Janairu zuwa Disambar shekarar.

Zazzagawa, ya alakanta raguwar masu mutuwa ta dalilin gobara a jihar da ayyukan wayar da kan jama’a da hukumar ta yi a shekarar 2019.

Daraktan ya kuma dora alhakin yawaitar samun gobarar kan yadda ake amfani da kayan lantarki ba bisa ka’ida ba, dawowar lantarkin da karfi, rashin iya amfani da abubuwa masu saurin kamawa da wuta, da kuma ayyukan injiniyoyin lantarki da ba su da kwarewa.

Zazzagawa, ya kuma shawarci mashaya taba sigari, su rika kashe wutar da zaran sun gama zukarta, don gujewa yaduwar gobarar musamman a wannan lokaci na hunturu.

Ya kuma bayyana bukatar da ke akwai na samun motoci masu aiki, domin samun damar kai dauki cikin gaggawa a duk inda aka samu tashin gobara a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply