Home Sabon Labari An sassauta dokar hana fita ta Kaduna

An sassauta dokar hana fita ta Kaduna

119
0

Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna @Samuel Aruwan ya sanar a yammacin Litinin din nan cewa daga ranar Talata mutanen da ke zaune a kananan hukumomi 21 na jihar za su iya fita neman halaliya a tsakanin karfe 6am zuwa karfe 4pm.

Sai dai Samuel Aruwan ya ce dokar hana fita ta awa 24 na nan na ci gaba da aiki a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun wadanda ke cikin garin Kaduna, amma sauran unguwannin garin Kaduna da ba sa cikin kananan hukumomin su an sassauta musu dokar. Kwamishinan ya ce dokar hana fita za ta ci gaba da aiki a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun domin duk da dokar da aka sanya wasu sun yi yunkurin ci gaba da wawusar kayan da ba nasu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply