Home Labarai An sauke sakataren gwamnatin Nasarawa

An sauke sakataren gwamnatin Nasarawa

149
0

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya sanar da sauke sakataren gwamnatin jihar Alhaji Aliyu Tijjani daga mukaminsa.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakatare a gidan gwamnatin jihar, ta ce gwamnan ya umurci sakataren gwamnatin jihar da aka sauke da ya hannanta komai a hannun babban sakatare na ofishinsa.

Gwamna Abdullahi Sule ya yi godiya ga sakataren gwamnatin jihar mai barin gado, duk da dai bai bayyana dalilin sauke shi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply