Babban sufeton ‘yansanda na Nijeriya Muhammad Adamu, ya umurci da gaggauta janye duk wani jami’in dansandan da ke aiki tare da hukumar EFCC.
Jaridar Punch ta rawaito cewa umurnin ya nuna cewa da zarar an janye wadancan, a gaggauta maye gurbinsu da wasu.
Muhammad Adamu yace ya zama wajibi dukkanin ‘yansandan da aka janye daga EFCC su koma hedikwatar ‘yansanda ta Nijeriya a ranar Litinin da safe.
Kazalika, an ba da umurnin cewa kada a bar kowa ya shiga harabar hukumar EFCC idan ba ma’aikacin wurin ba.
