Home Coronavirus An shigo da rigakafin Covid-19 na bogi a Nijeriya – NAFDAC

An shigo da rigakafin Covid-19 na bogi a Nijeriya – NAFDAC

65
0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta ce ta samu rahoton shigo da rigakafin Covid-19 na bogi a Nijeriya.

Babbar Daraktar Hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana haka a lokacin da wani taron ‘yanjarida a ranar Juma’a.

NAFDAC ta yi gargadin kan shigo da rigakafin ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa bata karba ko amincewa da wani rigakafin Covid-19 daga masu samar da shi ba zuwa cikin kasar ba.

Adeyeye ta kuma yi gargadin cewa rigakafin na bogi zai iya haifar da cutuka masu kama da cutar Covid-19, tana mai cewa ko amintaccen rigakafin sai an sa ido kan sa, don gano matsalolin da ke tattare da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply