Home Labarai An shirya wa mata taron horaswa kan kula da iyali a Sokoto

An shirya wa mata taron horaswa kan kula da iyali a Sokoto

87
0

Ma’aikatar kula da harkokin mata da kananan yara tare da tallafin Spotlight Initiative, sun shirya wani taron horar da mata kan illolin dake tattare da cutar coronavirus da kuma illolin dake tattare da cutar yoyon fitsari da kuma yadda za su kare kan su daga wadannan cututtuka.

Horon dai na tsawon kwanaki biyar, zai kuma koyar da matan yadda za su rungumi sana’o’i, kama daga kiwon dabbobi, dinkin Tela, da sauran su don dogaro da kai.

Haka kuma za a horar da matan kan zakulo wadanda suka watsar da karatun Boko don mayar da su a makarantu su ci gaba.

Manufar horon dai ita ce ganin mata sun Sami lafiya, Ilimi, da kuma sana’o’i ta yadda za su kula da Iyali kasancewarsu jigo ga ci gaban iyali a cikin al’umma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply