A Juma’ar nan ne aka soma gyaran ido kyauta ga masu fama da lalurar ido a babban assibitin garin Yawuri da ke cikin jihar Kebbi.
Aikin dai zai kwashe tsawon kwanaki uku karkashin kulawar ma’aikatar lafiya ta jihar Kebbi tare da hadin guiwar Dr. Yusuf Tanko Sununu dan majalisar Tarayya mai wakiltar Ngaski da Yawuri a majalisar tarayya.
Al’umma da dama na fama da matsalolin ido a yankin, to amma kuma gudanar da irin wannan aikin kyauta, zai taimaka ainun ga al’umma da galibi masu fama da wannan matsalar masu karamin karfi ne.
