Bankin duniya tare da hadin guiwar hukumar kula da gyaran madatsun ruwa da zaizayar kasa wato NEWMAP sun soma aikin tantancewa don gina magudanan ruwa a wasu unguwannin dake Birnin Sakkwato a wani mataki na magance ambaliyar ruwa.
Unguwar Tudun Wada da Mabera da ke Birnin Sakkwato na daga cikin unguwannin da aka soma wannan aiki inda tuni aka fara tantance magidanta da aikin zai shafi gidajen su don biyan diyya.
Aikin dai na Bankin duniya da hadin guiwar NEWMAP zai laƙume Naira biliyan biyu da miliyan dari uku.
