Home Labarai An tabbatar da mutum biyu sun kamu da cutar Lassa a jihar...

An tabbatar da mutum biyu sun kamu da cutar Lassa a jihar Kebbi

69
0

Mutum biyu ne aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin lassa a jihar Kebbi.

Jami’in kula da barkewar  cutuka na jihar Dr. Assad Hassan ya bayyana haka.

Ya ce daga cikin mutum 12 da ake zargin sun kamu da cutar a wannan shekara, mutum 2 ne aka tabbatar da cutar a jikin su, yayin da ake jiran sakamakon gwajin wani guda.

Jami’in ya ce mutum biyu da suka kamu da cutar sun fito ne daga kananan hukumomin Kalgo da Birnin Kebbi, yayin da sauran mutane 9 aka tabbatar ba su dauke da cutar.

Dr. Hassan ya yi kira ga jama’ar jihar da kar su tashi hankulan su domin cutar tana da magani, su kuma yi kokarin kai rahoton duk wasu alamun bullar cutar ga cibiyar lafiya mafi kusa.

Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su kauracewa cin duk wani abun da bera ya taba, domin nan ne babbar hanyar kamuwa da cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply