Home Kasashen Ketare An tallafi Nijeriya da kayayyakin yakar corona

An tallafi Nijeriya da kayayyakin yakar corona

111
0

Nijeriya ta karbi gudunmawar wasu kayayyakin kula da lafiya na musamman da kungiyoyi ECOWAS da WAHO suka yi hadaka domin tallafawa kasar a shirin da ta ke na yakar annobar corona.

Kasar ta sami wannan tallafin ne daga kungiyar kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS da kuma takwararta kungiyar kula da lafiya ta kasashen na yammacin Afrika da ake yi wa lakabi da WAHO.

Kayayyakin sun hada na’urar nan ta taimakawa wajen yin numfashi da sinadaran wanke hannuwa da kuma takunkumin rufe baki da hanci da akalla kudin su za su kai Dalar Amurka milyan takwas.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yakar annobar corona wanda sakataren gwamnatin kasar ke jagoranta shi ne aka mika wa wannan kayayyaki a Abuja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply