Home Labarai An tsawaita kwamitin rikon kwaryar APC tare da rushe shugabannin jihohi

An tsawaita kwamitin rikon kwaryar APC tare da rushe shugabannin jihohi

75
0

Kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na kasa, ya gudanar da wani taron gaggawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya kara wa kwamitin rikon kwara na shugabancin jam’iyyar wa’adin watanni 6.

Kwamitin ya kuma rushe shugabannin jam’iyyar na runfuna, mazabu, kananan hukumomi, jihohi da mataki shiyyoyi, tare da umartarsu su kafa kwamitin rikon kwarya.

Kwamitin ya kuma bada umarnin bada damar tsaya wa takarar mukamai ga sabbin shigowa jam’iyyar ba tare da sharadin sai sun yi shekaru biyu cikin jam’iyyar ba, kamar yadda aka yi a baya ba.

Hakama, kwamitin zartaswar ya yi kira ga jam’iyyar adawa ta PDP, da kada ta sa siyasa ga matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta, a maimakon hakan  ya kamata su hada hannu da gwamnati domin kawo karshen matsalar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply