Home Coronavirus An tsawaita lokdawun a Kaduna, yayin da aka bar masu yankan farci...

An tsawaita lokdawun a Kaduna, yayin da aka bar masu yankan farci fita neman na cefane

115
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta tsawaita dokar hana fita a jihar da sati biyu.

Mataimakiyar gwamnan jihar Dr Hadiza Sabuwa Balarabe ta bayyana haka a ranar Talatar nan.

Dokar hana fita a jihar dai na ƙarewa ne a ranar Talatar, bayan gwamnatin jihar ta tsawaita ta da kwana 30 a ranar 26 ga watan Afrilu.

Dr Sabuwa, ta ce an tsawaita dokar ne domin ƙara tabbatar da kariyar jama’ar jihar.

Saidai a wannan sabon tsari, an ƙara tsawaita kwanakin fita domin cefane daga kwana biyu zuwa uku, sannan an bada izinin wasu daga cikin ƴan kasuwa da masu shaguna su buɗe.

Ranakun fitar sune Talata, Laraba da Alhamis, sannan an bada dama ga masu walda, gyaran takalmi, yankan farci da dai makamantan su fitowa din gudanar da sana’o’in su.

Saidai gwamnatin jihar ta ce makarantu, wuraren ibada da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply