Home Labarai An tseratar da mutum 39 tare da kashe yanbindiga 2 a Kaduna

An tseratar da mutum 39 tare da kashe yanbindiga 2 a Kaduna

138
0

Wata musayar wutar da aka yi tsakanin ƴanbindiga da jami’an tsaro a daren Lahadi ta yi sanadiyyar mutuwar matafiya 2 da ƴanbindiga 2 a kan hanyar Kaduna-Abuja da Kaduna-Zaria.

Rundunar ƴansanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar hakan, tana mai cewa ƴanbindiga sama da 40 ne suka mamaye hanyar tare da yin harbe-harbe.

Da yake bayar da jawabi, kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce jami’an soji sun cimma ƴanta’addan ne yayin da suke tsaka da harbin ababen hawan al’umma a Kwanar Tsintsiya kan hanyar Kaduna-Zaria a karamar hukumar Igabi.

Aruwan ya tabbatar da kisan ɗaya daga cikin ƴanta’addan yayinda, da yawa daga cikinsu suka tsere bayan an jikkatasu, hakanan kuma sojojin sun samu nasarar kubutar da mutane 39 daga hannun ƴanbindigar, wanda suka fito daga Sokoto a kan hanyarsu ta zuwa garin Onitsha.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply