Home Labarai An wanke mataimakin Ganduje daga zargin cin hanci

An wanke mataimakin Ganduje daga zargin cin hanci

130
0

Hukumar karbar korafe-korafen cin hanci ta jihar Kano, ta wanke mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna daga zargin badakalar kudi a ma’aikatar aikin gona ta jihar.

Mataimakin gwamnan shi ne kwamishinan aikin gona na jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa yanzu haka hukumar na bincikar babban sakatare da wani darakta da karin wasu ma’aikata bisa zargin karkatar da wasu kudade.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta ce ta karbo kudi Naira milyan 7,150,000 daga cikin kudin da aka karkatar.

Bayan wanke mataimakin gwamnan, shugaban hukumar Muhuyi Magaji RiminGado a cikin wata takarda, ya ce sun gano cewa babu hannun mataimakin gwamnan a wannan badakalar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply