Home Sabon Labari ANYI AURE DA MARA KWABO: Tambuwal ya fara biyan albashin Naira 30...

ANYI AURE DA MARA KWABO: Tambuwal ya fara biyan albashin Naira 30 a Sakkwato

84
0

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya cika alkawarin fara biyan dubu talatin a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Wakilinmu na jihar Sakkwato ya ce yanzu haka dai  ma’aikatan jihar Sakkwato na cike da zumudi da murna kan wannan matakin da gwaman ya dauka. Kuma tuni wasunsu sun fara jin “alert”, wato, shigowar sabon albashin a asusun na banki a ranar Talata da daddare.

Dama dai a ‘yan makonnin da suka gabata ne Gwamnan ya kaddamar da dokar fara biyan dubu talatin mafi karancin albashi a jihar Sakkwato, inda ya nuna za ta soma aiki a karshen wannan wata na Janairu. Sai ko gashi alkawarin ya ya tabbata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply