Home Labarai An yi garkuwa da jami’in hukumar “Immigration”

An yi garkuwa da jami’in hukumar “Immigration”

218
0

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka gidan wani jami’in hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS), Salisu Usman, a garin Gudi da ke karamar hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa, inda suka sace shi tare da matarsa.

Daily Trust, ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun samu damar shiga cikin gidan jami’in ne bayan da su ka razana matasan da ke kusa da gidan, kana daga bisani suka afka gidan inda suka sace jami’in da matar sa.

Shi dai wannan jami’i da aka yi garkuwa da shi, shaidu sun tabbatar da cewa dan’uwan ne ga tsohon ministan watsa labarai a lokacin gwamnatin da ta gabata, Labaran Maku.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply