Home Labarai An yi jana’izar Abba Kyari

An yi jana’izar Abba Kyari

103
0

Rahotanni daga Abuja na cewa an yi jana’izar Malam Abba Kyari a gidansa sa ke cikin gidajen jamian tsaro da akafi sani da Defence House.

Fadar gwamnatin shugaban kasar Nijeriya ta sanar da rasuwar Shugaban ma’aikatan ta Malam Abba Kyari a daren ranar Asabar.

Femi Adesina wanda shi ne mai taimaka wa shugaban kasar Nijeriya ta hanyar yaɗa labarai ya sanar da mutuwar a shafinsa na Twitter.

Kyari ya rasu ne a wani asibiti dake birnin Legas inda yake jinya.

Tun a ranar 24 ga watan Maris ne aka fitar da sanarwa Abba Kyari ya harbu da cutar Coronavirus bayan dawowarsa daga ƙasar Jamus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply